Euro 2020: Ɗan wasan Denmark Christian Eriksen da ya some a fili ya farfaɗo

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Denmark ta ce ɗan wasanta Christian Eriksen ya farfaɗo bayan ya some a fili.

Ɗan wasan ya faɗi ana tsakiyar wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2020.

Ɗan wasan ya faɗi ne shi kaɗai ba ƙwallo tare da shi a yayin da ƙasarsa Denmark ke tsakiyar fafatawa da Finland a ranar Asabar.

Sanarwar da hukumar ƙwallon Denmark ta fitar ta ce "Christian Eriksen ya farfado kuma yana samun sauƙi amma har yanzu yana kwance a asibiti"

Amma an kwashi ɗan wasan some a filin wasa, al'amarin da ya sa aka dakatar da wasan. Abokan wasansa dukkaninsu sun fice fili suna ƙwalla, wasunsu kuma suna ta addu'a.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai Uefa ta ce an ci gaba da wasan ne bayan tattaunawa da hukumomin Denmark da Finland.