Real Madrid ta dauki Carlo Ancelotti a karo na biyu

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta sanar ranar Talata cewar ta dauki Carlo Ancelotti a karo na biyu da zai ja ragamar kungiyar.
Dan kasar Italiya ya fara jan ragamar Real tsakanin 2013 zuwa 2015, wanda ya lashe Champions League a kakarsa ta farko a kungiyar.
Ancelotti zai maye gurbin Zinedine Zidane wanda ya ajiye aikin cikin watan nan, bayan da Real Madrid ba ta lashe kofi ba a 2020/21.
Ancelotti na aiki a Goodison Park tare da Everton tun daga Disambar 2019 kan kwantiragin shekara hudu da rabi.
Everton ta karkare kakar Premier ta bana a mataki na 10 a teburi da maki 59, iri daya da na Leeds wadda ta yi ta tara.
Dan kasar Italiya wanda ya horar da kungiyoyin Turai da yawa ya lashe Champions League a kakar farko da ta ci kofi na 10 a tarihi daga baya aka sallame shi wata 12 tsakani.
Ancelotti yana daga cikin koci uku da ya hada da na Liverpool, Bob Paisley da Zidane da suka ci ko dai European Cup ko kuma Champions League uku.
Ya kuma ja ragamar AC Milan ta lashe babbar gasar Zakarun Turan a 2003 da kuma 2007.
Ancelotti ya horar da Juventus da Chelsea da Paris St Germain da kuma Bayern Munich a shekara 26 da ya yi yana horar da tamaula.
Kocin zai rattaba kwantiragi a kungiyar, sannan a gabatar da shi a gaban 'yan jarida ranar Laraba.










