Bayern Munich ta kori Carlo Ancelotti

Carlo Ancelotti

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kocin mai shekara 58 ya jagoranci Real Madrid tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta sallami kocinta, Carlo Ancelotti, kwana guda bayan ta yi rashin nasara a hannun Paris St-Germain (PSG).

A ranar Laraba ne PSG ta doke Bayern da ci 3-0.

Ancelotti ya maye gurbin Pep Guardiola ne a kakar bara.

Ancelotti dan asalin Italiya ya taimaka wa Bayern ta lashen kofin Bundesliga a baya, amma kuma kungiyar ta iya kai wa wasan gab da na kusa da na karshe a kasar Zakarun Turai.

Mataimakinsa Willy Sagnol ne zai maye gurbinsa a matsayin kocin wucin gadi.