Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kane, Buendia, Sule, Aguero, Pjanic, Giroud, Guedes

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta shirya tsaf domin yi wa Manchester United da Chelsea kwacen Harry Kane - dan wasan gaba mai shekara 27, wanda ya kafe kungiyar Tottenham ba ta isa ta hana shi tafiya ba. (Star)
'Yan wasan Spurs sun kadu matuka da matakin da Kane ya dauka na bayyanawa karara ya na son barin kungiyar. (Mirror)
Arsenal na kokarin dauko dan wasan tsakiya dan Agentina Emiliano Buendia mai shekara 24, daga Norwich City, yayin da Gunners ke kokarin maye gurbin dan wasan Norway Martin Odegaard, mai shekara 22, wanda zai koma Real Madrid a karshen kakar wasanni a matsayin dan aro. (Mail)
Zakarar gasar Premier League wato Manchester City, ta shirya domin ba dan wasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 26, sabuwar kwantiragi mai tsaho. (Telegraph, subscription required)
Dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 31, ka iya tsawaita kwantiragin aro a kungiyar Tottenham da karin shekara daya, idan aka bai wa dan wasa Harry Kane damar ficewa daga kungiyar. (AS)
West Ham da Fulham sun shirya domin rattaba hannu kan dauko dan wasan gaba na Blackburn Rovers Adam Armstrong, mai shekara 24-wanda darajarsa ta kai fam miliyan 25m, sai dai duka kungiyoyin biyu na fuskantar barazana daga kungiyoyin Brighton da Everton kan cinikin dan wasan. (Sun)
West Bromwich Albion za su fara tattaunawa da tsohon manajan Sheffield United Chris Wilder, mai shekara 53, domin ya maye gurbin mai horas da 'yan wasan kungiyar Sam Allardyce. (Telegraph, subscription required)
Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ci gaba da nuna sha'awar dauko dan wasan baya naBayern Munich da Jamus Niklas Sule, mai shekara 25. (Abendzeitung - in German)
Manchester United ta nuna wa FC Nordsjaelland karara, ta na shirin dauko dan wasan Ajax dan kasar Ghana Kamaldeen Sulemana mai shekara 19. (Football Insider)











