An tuhumi Chelsea da Leicester da halin rashin da'a

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi Chelsea da Leicester City da halin rashin da'a, sakamakon yamutsi da aka yi tsakanin 'yan wasa da jami'an kungiyoyin a gasar Premier League.
Lamarin ya faru ne daf da za a tashi daga wasan da suka kara ranar Talata fafatawar mako na 37 a gasar ta Ingila, inda Chelsea ta yi nasara da ci 2-1.
Sakamakon wasan ne ya kai Chelsea mataki na uku a kan teburin Premier League da maki 67, inda Leicester City mai maki 66 ta koma ta biyar, bayan da Liverpool ta doke Burnley da ci 3-0 ranar Laraba.
Leicester ta yi nasarar doke Chelsea a King Power a wasan farko a Premier bana cikin watan Janairu, sannan ta lashe FA Cup bayan cin kungiyar Stamford Bridge 1-0 a Wembley.
Chelsea za ta buga wasan karshe a Champions League da Manchester City ranar 29 ga watan Mayu a Portugal.
An bai wa kungiyoyin zuwa 25 ga watan Mayu domin su kare kansu.
Ranar Lahadi za a karkare kakar bana, inda Leicester City za ta karbi bakuncin Tottenham, ita kuwa Chelsea gidan Aston Villa za ta je.






