Leicester City ta casa Liverpool

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Leicester City ta dawo matsayi na biyu a teburin Premier bayan ta doke Liverpool 3-1 a karawar da suka yi ranar Asabar.

Liverpool ce ta fara ci inda Salah ne ya fara buɗe raga ana minti 67 da wasa amma kuma a minti 78 Maddison ya farke wa Leicester a bugun tazara.

Vardy da Barnes suka ci wa Leicester City sauran ƙwallayen a ragar Liverpool cikin minti takwas.

Yanzu Leicester City tana matsayi na biyu a tebur da maki 46 tazarar maki huɗu tsakaninta da Manchester City da ke shirin karɓar baƙuncin Tottenham.

Liverpool mai riƙe da kofin gasar kuma tana nan a matsayi na huɗu da maki 40 tazarar maki 10 tsakaninta da Man City.

Idan Man City da ke da kwanten wasa ta doke Tottenham zai kasance tazarar maki 13 ta ba Liverpool.