Real Madrid ta barar da damar hawa teburin La Liga

Real Madrid vs Sevilla

Asalin hoton, Getty Images

Real ta sha da kyar a hannun Sevilla a wasan mako na 35 da suka fafata a gasar La Liga a Alfredo Di Stefano, bayan da suka tashi 2-2.

Minti 22 da fara wasa ne Sevilla ta ci kwallo ta hannunFernando Reges, kuma haka suka kammala minti 45 da wannan sakamakon.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Real ta farke ta hannun Marco Asensio.

Daga baya ne Sevilla ta kara na biyu ta hannun Ivan Rakitic a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Daf da za a tashi daga karawar Real ta farke na biyu ta hannun Diego Carlos wanda ya ci gida.

Da wannan sakamakon Rel ta koma mataki na biyu a kan teburi da maki 75, iri daya da na Barcelona ta uku a teburi.

Ranar Asabar Barcelona da Atletico Madrid suka tashi 0-0 a Camp Nou, hakan ya sa Atletico ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 77.

Ita kuwa Sevilla tana ta hudu a teburin da tazarar maki hudu tsakaninta da Real Madrid da kuma Barcelona.

Kawo yanzu saura wasa uku-uku a karkare gasar ta Spaniya ta bana.

Wasannin mako na 36 da za a buga:

Talata 11 ga watan Mayu

  • Osasuna da Cadiz
  • Elche da Deportivo Alaves
  • Levante da Barcelona

Laraba 12 ga watan Mayu

  • Sevilla da Valencia
  • Celta Vigo da Getafe
  • Huesca da Athletic Bilbao
  • Atletico Madrid da Real Sociedad

Alhamis 13 ga watan Mayu

  • Real Valladolid da Villarreal
  • Eibar da Real Betis
  • Granada da Real Madrid