La Liga: Real Madrid ta kara tazara a saman teburi

Asalin hoton, @realmadriden
Real Madrid ta bai wa Barcelona tazarar maki uku a saman teburin La Liga sakamakon nasarar da ta yi a kan Deportovo Alaves da ci 1-2.
Tawagar Zinedine Zidane ta samu kwallon farko ta kafar kyaftin kuma bangonta wato Sergio Ramos a minti na 52 bayan wani bugun tazara da Kroos ya bugo, inda ya saka mata kai kamar yadda ya saba.
Minti 12 bayan haka Perez ya farke ta daga bugun finareti sakamakon ketar da Ramos ya yi wa Joselu a cikin yadi na 18 kuma aka ba shi katin gargadi.
Dani Carvajal ne ya bai wa masu ziyarar nasara da kwallon da ya ci a minti na 69.
Babbar abokiyar hamayyarta Barcelona ka iya kamo ta idan har ta samu nasara a wasan hamayya da za ta ziyarci Atletico Madrid da karfe 9:00 na daren Lahadi.







