Arsenal: Yau ma ba ta sauya zani ba

Asalin hoton, Getty Images
Mai horarwa na rikon kwarya Freddie Ljunberg bai iya sauya sakamakon da Arsenal ta rika samu ba a baya-bayan nan sakamakon canjaras da ta buga 2-2 a filin wasa na Carrow Road.
Arsenal ba ta yi nasara ba a cikin wasa shida a jere da ta buga a Premier - canjaras hudu, rashin nasara biyu - wanda shi ne mafi dadewa da ta yi a tarihinta tun a Disamban 1994 a karkashin mai horarwa George Graham.
Norwich City ba ta bari wasa ya ci ta ba duk da cewa a gidanta aka fafata, wanda Aubameyang ya ci wa tagawar Gunners kwallo biyu.
Norwich din ce ta fara jefa kwallo ta kafar Teemu Pukki a minti na 21 kafin Aubameyang ya farke ta a minti na 29.
Aubameyang ne ya kara farke wa Arsenal kwallonta daga bugun finareti a minti na 57 bayan Cantwell ya kakaba mata a minti na 45+2. Sau biyu aka buga finaretin, inda VAR ta ce golan ya fita daga layi kafin Aubameyang ya buga.
Kwallo 10 kenan Aubameyang ya ci a Premier ta bana, wanda kuma shi ne ya ci gaba da jagorancin 'yan wasan Arsenal a cikin fili wato kyaftin.
Wannan sakamkaon ya mayar da Arsenal ta takwas a teburi da maki 19.


