Chelsea 2-5 West Brom: Karon farko an doke Thomas Tuchel a Chelsea

Karon farko an doke Thomas Tuchel a matsayinsa na kocin Chelsea bayan West Bromwich Albion ta yi masa ci 5-2 a Stamford Bridge.

Chelsea ta ƙare wasan ne da ƴan wasa 10 bayan an bai wa Thiago Silva jan kati.

Tuchel ya buga wasa 14 ba a doke shi ba a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar, bayan Chelsea ta kori Frank Lampard a watan Janairu.

Ɗan wasan Chelsea Christian Pulisic ne ya fara ziyara ƙwallo a raga, kafin a bai wa Thiago jan kati.

Ana dab da zuwa hutun rabin lokaci ɗan wasan Albion Matheus Pereira ya ci ƙwallaye biyu, ya zama ana nasara kan Chelsea da ci 1-2.

Mbaye Diagne ya ci wa West Brom ƙwallo ta uku yayin da kuma Callum Robinson ya rufe da sauran ƙwallayen a ragar Chelsea.

Sakamakon wasan wani ƙalubale ne ga fafutukar da Chelsea take na yi ƙare gasar a cikin jerin huɗun farko domin samun gurbin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai.

Wannan ne karon farko da aka ci Chelsea ƙwallaye biyar tun 2011 da Arsenal ta zazzaga mata ƙwallayen.