Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tuchel zai fuskanci kalubalen da zai fayyace kwazonsa a Chelsea
Thomas Tuchel ya ja ragamar Chelsea karawa takwas, wanda ya ci wasa shida da canjaras biyu, tun bayan da ya koma kungiyar cikin watan Janairu.
Sai dai kocin yana da wasa biyar a jere da zai fafata wanda zai zamar masa zakaran gwajin dafi a zuwansa Ingila horar da tamaula.
A makon jiya kocin ya buga 1-1 da Southampton a gasar Premier League da hakan ya hana shi kai wa cikin 'yan hudun farko a gasar.
Sai dai Tuchel ya nuna da gaske yake, bayan da ya je ya doke Atletico Madrid 1-0 a wasan zagaye na biyu karawar farko a gasar Champions League.
Ranar Lahadi Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United ta biyu a teburin Premier da za su fafata a Stamford Bridge.
Bayan United kungiyar ta Stamford Bridge za ta kara da Liverpool da Everton da kuma Leeds United a gasar Premier.
Wasa na biyar shi ne neman zuwa fafatawar Quarter finals idan ya karbi bakuncin Atletico a wasa na biyu a Champions League.
Chelsea tana ta biyar a teburin Premier League da maki 43 daga karawa 25 da ta yi a gasar da tazarar maki biyu tsakaninta da West Ham ta hudu.
Chelsea na fatan kammala gasar bana ta Premier League cikin 'yan hudun farko, sannan ta taka rawar gani a Champions League.
Tuchel ya maye gurbin Frank Lampard a lokacin da kungiyar ke ta tara a teburin Premier League.
Kalubale biyar da ke gaban Chelsea:
Premier League 28 ga watan Fabrairu 2021
- Chelsea da Man United
Premier League 4 ga watan Maris 2021
- Liverpool da Chelsea
Premier League 8 ga watan Maris 2021
- Chelsea da Everton
Premier League 13 ga watan Maris 2021
- Leeds da Chelsea
Champions League 17 ga watan Maris 2021
- Chelsea da Atletico Madrid