Tuchel da Dortmund sun raba gari

Kocin Borussia Dortmund, Thomas Tuchel ya bar kungiyar bayan shekara biyu yana gudanar da aiki.

Tuchel mai shekara 43, ya koma horar da Dortmund a shekarar 2015, bayan da Jurgen Klopp ya koma jan ragamar Liverpool.

Tuchel ya bar Dortmund ne bayan da dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da babban jami'in kungiyar Hans-Joachim Watzke kan harin ta'addanci da aka kai wa kungiyar a ranar 11 ga watan Afirilu.

Sai dai kungiyar ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce kocin ya bar Dortmund ne don radin kansa, babu tantama a tsakaninsu.

A ranar Asabar Dortmund ta lashe kofin kalubalen Jamus, bayan da ta doke Eintracht Frankfurt.

Haka kuma kungiyar ta kare a mataki na uku a gasar Bundesliga ta kakar nan, hakan ya sa kungiyar za ta buga Gasar Zakarun Turai mai zuwa.