Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Atletico ta bayar da tazarar maki bakwai a La Liga
Atletico Madrid ta bayar da tazarar maki bakwai a teburin La Liga, bayan da ta doke Valencia da ci 3-1 a karawar da suka yi ranar Lahadi.
Valencia ce ta fara cin kwallo a minti na 11 da fara tamaula ta hannun Uros Racic, yayin da Atletico ta farke ta hannun Joao Felix minti 12 tsakani.
A minti na 54 ne tsohon dan kwallon Barcelona, Luis Suarez ya ci wa Atletico na biyu kuma na 12 a bana da hakan ya say a yi kan-kan-kan da Youssef En-Nesyri shima mai kwallo 10 a raga.
Saura minti 12 a tashi daga karawar Angel Correa ya kara kwallo na uku a ragar Valencia da hakan ya bai wa Atletico nasarar cin wasa bakwai.
Atletico mai kwantan wasa tana da maki 47, sai Real Madrid ta biyu mai maki 40, sannan Barcelona mai 37.
Ita kuwa Valencia tana ta 14 a kasan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da 'yan ukun karshen teburi.