Luis Suarez na bude wuta a Atletico Madrid a bana

Luis Suarez na taka rawar gani a Atletico Madrid a kokarin lashe kofin La Liga a bana.

Tun bayan da dan wasan ya koma kungiyar daga Barcelona a bana ya ci kwallo 11 kawo yanzu.

Ya zuwa yanzu maki bakwai Atletico ta barar a La Liga ta bana, bayan cin wasa 14 da canjaras biyu da rashin nasara daya a karawa 17 a gasar.

A baya-bayan nan sai cin kwallaye yake yi, wanda ya zura biyu a ragar Elche a wasan da suka yi nasara da ci 3-1.

Ya kuma ci Getafe kwallo da Alaves da biyun da ya zura a ragar Eibar a wasan da Atletico ta yi nasara da ci 2-1.

Dan wasan tawagar Uruguay ya ci kwallo shida a karawa shida baya da ya yi da hakan ya bai wa Atletico hada maki bakwai a gasar ta La Liga.

A bara a irin wannan lokaci wasa bakwai Atletico ta yi nasara tana ta biyar a teburin La Liga da tazarar maki bakwai tsakaninta da wadda take ta daya a lokacin.

Kawo yanzu Atletico ta ci wasa 13 daga 14 da ta buga kuma ba a doke ta ba tun cikin watan Disambar 2019.

Watakila Luis Surez ya lashe kofin La Liga a Atletico a karon farko da ya koma kungiyar daga Barcelona wadda take ta uku a teburi.

Atletico ce ke jan ragamar teburin La Liga da kwantan wasa biyu kuma.