FA Cup: Manchester United ta kara yaga ɓarakar Liverpool

Kyakkyawan bugun tazarar da Bruno Fernande ya ci a minti na 78 ya bai wa Manchester United nasarar kora Liverpool gida a gasar FA.

Wasan hamayyar da ka buga tsakanin kungiyoyin biyu ya fara ne da zira kwallo a ragar United ta hannun Mohamed Salah, hakan ya bai wa Liverpool damar jan ragamar wasan a filin wasa na Old Trafford.

Salah ne dai ya farke kwallo ta biyu da Liverpool ta ce, bayan Mason Greenwood ya farke wa Manchester Marcus Rashford kuma ya kara.

Nasarar da United ta yi a wannan zagayen zai ba ta damar tsallakawa zagaye na biyar a gasar, inda za ta hadu da West Ham kungiyar tshon kocinta David Moyes.

Wannan ne wasa na biyu da su kara tsakaninsu a bana, bayan tashi 0-0 da suka yi a gasar Premier ranar 17 ga watan Janairu a Anfield.

Manchester United tana mataki na daya a kan teburin Premier League da maki 40, ita kuwa Liverpool mai rike da kofin tana ta hudu da maki 36.

Sai dai wannan wasan na FA Cup da za su buga zai auna kokarin Liverpool, bayan da rabon da ta yi nasara a Old Trafford tun 3-0 a Maris din 2014.

Burnley ce ta fara yaga ɓarakar Liverpool a gasar Premier har filin wasa na Anfield, wanda rabon da a ci Liverpool a cikinsa tun 2017.

Sau nawa suka fafata a FA Cup?

Kungiyoyin sun kara a FA Cup sau 17 har da wanda suka hadu karo biyu a karni na 19 a lokacin da ake kiran Manchester United da sunan Newton Heath.

United ta ci wasa tara da canjaras hudu, Liverpool ta yi nasara a hudu.

Wasan da Liverpool ta yi nasara a gidan Manchester United shi ne a shekarar 1921.

Kwazon da Manchester United ta yi a FA Cup

United ta yi nasara a wasa bakwai baya da ta yi a gida ba tare da an zura mata kwallo a raga ba.

Dan wasan da ya je Old Trafford ya ci kwallo a FA Cup shi ne Dimitri Payet cikin watan Maris 2016

Rabon da United ta yi rashin nasara a zagaye na hudu a FA Cup tun bayan nasarar da Liverpool ta yi a 2012.

United mai FA Cup 12 na kai wa Quarter finals a kaka shida a jere, tun bayan da Swansea ta doke ta a zagaye na uku a 2014.

Kokarin Liverpool a FA Cup

Sau biyu Liverpool ta kai Quarter finals, tun bayan da ta lashe kofin a 2006.

Liverpool ta kasa haura karawar zagaye na hudu a kaka biyar da Jurgen Kloop ke jan ragama.

Sun ci kwallo a wasa 15 daga 17 da suka yi a waje a FA Cup.

Liverpool ta yi nasara a wasa uku baya a bugun fenariti a FA Cup ne.