Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mesut Ozil ya ce shi dan Arsenal ne har abada
Mesut Ozil ya ce shi dan Gunners ne har abada, bayan da ya kammala komawa Fenerbahce da taka leda, daga Arsenal.
Mai shekara 32 tsohon dan kwallon tawagar Jamus ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku da rabi da kungiyar da ke buga gasar Turkiya.
Ya lashe FA Cup uku a Arsenal ya kuma ci kwallo 44 a wasa 254 da ya yi wa kungiyar a dukkan fafatawa, sai dai rabon da ya buga mata tamaula tun cikin watan Maris din 2020.
Ozil ya fadi cewa ''Abu ne mai wahala na bayyana yadda nake kaunar Arsenal da magoya bayanta''
"Ta ya ya zan iya kwatanta shekara takwas da na yi a kungiyar cikin kalami?
"Kawai ni dan Gunners ne har abada - ba wata tantama''
Ozil ya koma Emirates da taka leda daga Real Madrid kan kudi fam miliyan 42.4 a shekarar 2013, a matsayin wanda ta dauka mafi tsada a lokacin.
Ya kuma fara da kafar dama, domin kungiyar ta lashe FA Cup, a lokacin shekara tara rabonta da shi.
Ya buga wasa 32 a kakar 2014-15 sakamakon jinyar wata shida, sannan ya lashe FA Cup a kaka ta biyu a jere.
Ozil ya zama dan wasan da aka fi biyan albashi mafi tsoka a Arsenal a Janairun 2018, bayan da ya tsawaita zamansa a kungiyar shekara uku da rabi kan fam 350,000 a ko wanne mako.
Unai Emery ne ya fara kin saka Ozil a wasa daga baya ya ci gaba da murza leda karkashin Freddie Ljungberg.
Bayan da aka nada Mikel Arteta kocin Arsenal a Disambar 2019, ya ci gaba da sa Ozil a wasa, wanda ya buga karawa Premier League 10 kafin bullar cutar korona.
Cikin watan Oktoba ne Arteta bai saka sunan Ozil cikin yan wasa 25 da za su buga wa Gunners European Cup da kuma Premier League ba.