Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Aguero, Alaba, Dembele, Benitez, Ings, Sanson, En-Nesyri da Palmieri

Barcelona na fatan daukar dan wasan Manchester City Sergio Aguero, mai shekara 32, da takwaransa na Bayern Munich David Alaba, mai shekara 28, a bazara idan kwangilar kowannensu ta kare. (Mundo Deportivo, via Mail on Sunday)

Chelsea da Manchester United na sanya ido kan halin da dan wasan Faransa Ousmane Dembele yake ciki a Barcelona, a yayin da ya rage wata 18 kwangilar dan wasan mai shekara ta kare ta Nou Camp. (Sport, via Metro)

KocinBarcelona Ronald Koeman ya san cewa "halin da tattalin arzikin kungiyar yake ciki yana da tasiri" kan yunkurin da yake na sayen 'yan wasa sai dai ya ce akwai bukatar kungiyar ta dauki karin 'yan wasa idan tana so ta inganta yadda take murza leda. (Goal)

Kocin Leicester City Brendan Rodgers na cikin koci-koci da Chelsea za ta so dauka domin maye gurbin Frank Lampard idan ta kore shi daga aiki. (Daily Star on Sunday)

Everton da Leicester City na son daukar dan wasan Southampton da Ingila Danny Ings, wanda saura wata 18 kwantaraginsa ta kare. (90 Min)

Tsohon kocin Liverpool da Newcastle United Rafael Benitez yana son komawa fagen horas da 'yan kwallo cikin gaggawa bayan da ya bar kungiyar Dalian Professional ta kasar China, kuma rahotanni sun ce Napoli da Roma na zawarcin kocin dan kasar Sifaniya mai shekara 60. (Sunday Times - subscription required)

Manchester United za ta yanke shawara kan makomar dan wasan Ingila Jesse Lingard bayan sun fafata da Liverpool a gasar cin Kofin FA, inda aka ce Newcastle United, Sheffield United da kuma West Brom suna son karbar aron dan wasan mai shekara 28. (Mail on Sunday)

Ana rade radin cewa West Ham na zawarcin dan kasar Morocco Youssef En-Nesyri amma dan wasan mai shekara 23 ya ce ba zai bar Sevilla a watan Janairu ba. (Estadio Deportivo, via Sport Witness)

Kazalika West Hamza ta yi yunkurin daukar dan wasan Celtic Odsonne Edouard mai shekara 23 a wannan watan sai dai dan kasar Faransa ya fi so ya tafi daya daga cikin manyan kungiyoyi shida da ke buga Premier League. (Daily Star on Sunday)

Aston Villa ta sake tsara kwangilar dan wasan Marseille Morgan Sanson kuma tana dab da kammala tattara £15.5m domin dauko dan wasan dan kasar Faransa mai shekara 26. (Mail on Sunday)

Chelsea ta yi watsi da tayin West Ham kan dan wasan Italiya mai shekara 26 Emerson Palmieri. (Sunday Mirror)

Bayern Munich ta soma samun ci gaba a game da tattaunawar da take yi da dan wasa Jamal Musiala mai shekara 17 a yayin da ake rade radin cewa Liverpool da Manchester United suna sanya ido kan dan wasan na Ingila da ke murza leda a rukunin 'yan kasa da shekara 21. (Goal)