Barcelona da Real Madrid sun mayar da hankali kan Copa del Rey

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona da Real Madrid sun yi asarar Spanish Super Cup a bana, wanda ya kamata daya daga cikinsu ta lashe don bunkasa wasanninta.

Real ce mai rike da kofin da ta lashe a bara a Saudi Arabia kuma na 11 jumulla, inda Athletic Bilbao ta fitar da ita a bana.

Barcelona mai rike da Spanish Super Cup 13 jumulla ta sha kashi a hannun Athletic Bilbao da ci 3-2 duk da karin lokaci.

Wannan ne karo na uku da Athletic ta yi nasarar lashe Spanish Super Cup.

Yanzu dai kofin da kungiyoyin Spaniya ke hari shi ne Copa del Rey da ya kamata Barcelona da Real Madrid za su buga ranar Laraba da Alhamis.

Gasar Copa del Rey Laraba 20 ga watan Janairu

Cordoba da Real Sociedad

Alcoyano da Real Madrid

Gasar Copa del Rey Alhamis 21 ga watan Janairu

UD Ibiza da Athletic Bilbao

Cornella da Barcelona

Valencia ce ke rike da Copa del Rey na 2018/19, bayan da ba a buga wasan karshe a kofin bara ba tsakanin Real Sociedad da Athletic Bilbao, saboda koma baya da cutar da korana ta haddasa.

Barcelona ce kan gaba wajen yawan lashe Copa del Rey mai 29, sai Athletic Bilbao 22 da kuma Real Madrid mai 19 jumulla.

Kofin gasar La Liga

Sai a ranar Laraba 23 Real Madrid za ta ziyarci Deportivo Alaves a wasan mako na 20 a gasar La Liga.

Ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Elche ranar Alhamis 24 a wasan na mako na 20 a gasar ta kasar Spaniya.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburi da maki 37, Barcelona mai maki 34 tana biye da Real.

Atletico mai kwantan wasa biyu ce kan gaba a teburin La Liga mai maki 41.

Real Madrid ce mai rike da kofin La Liga, yayin da Barcelona ba ta ci kofi ko day aba a kakar bara.

Gasar Champions League

Haka kuma kungiyoyin biyu na Spaniya sun kai karawar zagaye na biyu a Champions League na bana.

Ranar 16 ga watan Fabrairu, Barcelona za ta karbi bakuncin Paris St Germain, yayin da Real Madrid za ta ziyarci Atalanta ranar 24 ga watan Fabrairun.