Shekara 10 kenan da Barcelona ta mamaye kyautar Ballon d'Or

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 10 ga watan Janairun 2011, 'yan wasan Barcelona suka zama kan gaba a jerin wanda zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya wato Ballon d'Or.
Lionel Messi ne ya zama zakara a shekarar, yayin da takwaransa Xavi Hernandez ya yi na biyu, sai Andres Iniesta da ya yin na uku.
A lokacin Barcelona tana kan ganiya domin wata shida tsakani ta lashe Champions League kuma na hudu a tarihin kungiyar.

Asalin hoton, Getty Images
Messi ya fara lashe kyautar Ballon d'Or a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.
Barcelona wadda ke fuskantar kalubale a kakar bana tana ta uku a kan teburin La Liga da maki 34.
Atletico c eke jan ragama da maki 38 da kwantan wasa uku, sai Real Madrid ta biyu da maki 37.
Ranar Asabar Barcelona ta je ta casa Granada a wasan mako na 18 da ci 4-0,







