Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar Cinikin 'yan wasa: Makomar Messi, Camavinga, Ramos, Alaba, James
Manchester City ta dage sai Lionel Messi mai shekara 33, dan wasan Argentina da Barcelona ya koma kungiyar bayan da tsohon kocinsa Pep Guardiola ya sabunta kwantiraginsa a kungiyar. (Mirror)
Manchester United tana takara da Paris St-Germain da Real Madrid domin sayen Eduardo Camavinga, dan wasan tsakiya na Faransa da Rennes mai shekara 18. (Marca, via Mail)
Wasu kungiyoyin Gasar Firimiyar Ingila na son sayen Sergio Ramos, dan wasan baya na Real Madrid mai shekar 34 idan ya ki sabunta kwantiraginsa da kungiyar. (90min)
Real Madrid na son sayo David Alaba dan wasan baya na Bayern Munich da Austria mai shekara 28 ko Ramos ya bar kungiyar ko ya ci gaba da zama. (Marca)
Everton na neman Danie James, dan wasan gefe na Manchester United da kasar Wales mai shekara 23 a watan Janairu. (Football Insider)
Dan wasan gaba na Chelsea Oliver Giroud mai shekara 34 yana son barin kungiyar a watan Janairu domin ya ci gaba da zama cikin 'yan wasan Faransa da za su wakilci kasarsa a gasar Zakarun Turai. (Guardian)
Newcastle United ta ce a shirye take ta karbi tayi daga kungiyoyi masu sha'awar sayen dan wasanta na tsakiya Miguel Almiron mai shekara 26 wanda tuni wasu kungiya suka dade suna zawarcinsa. (90min)
Dan wasan Juventus da kasar Jamus Sami Khedira mai shekara 33 na son komawa Gasar Firimiyar Ingila tare da Everton ko Manchester United. (Sun)
Attajirin nan dan Najeriya Orji Kalu na son sayen kashi 33 cikin 100 na hannun jari a kungiyar Arsenal kuma yana son kungiyar ta dawo kan ganiyarta ta lashe gasa daban-daban. (Mirror)
Dan wasan baya na Arsenal da Brazil, David Luiz mai shekara 33 ya kara da Dani Ceballos yayin da suke atasaye kuma ya daki dan wasan Sfaniyan mai shekara 24 a hanci. (The Athletic - subscription required)