Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi ko zai iya barin Barcelona a watan Janairun badi?
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
A cikin watan Agusta Manchester City ta so daukar Lionel Messi daga Barcelona, bayan da dan kwallon ya bukaci barin camp Nou.
Barcelona ta ci karo da cikas a bara, bayan da ta kasa lashe kofi, bayan dukan kawo wuka da Bayern Munich ta yi mata a Champions League.
Kyaftin din tawagar Argentina ya samu rashin jituwa da Josep Bartomeu - wanda ya ajiye aikin shugabantar Barcelona a cikin watan Oktoba.
Kwantiragin Messi zai kare a Camp Nou a karshen watan Yunin 2021, wanda hakan na nufi wata kungiyar za ta iya tattaunawa da shi da nufin daukar shi ranar 1 ga watan Janairu.
Wannan dama ce idan Manchester City za ta yi amfani da ita wajen sake zawarcin kyaftin din Argentina.
Wasu bayanai na cewa City za ta iya biyan Barcelona Yuro miliyan 50, kunɗin da kungiyar za ta amince saboda halin matsi da cutar korona ta haddasa.
Idan ba haka ba City za ta iya jira zuwa karshen kakar bana, lokacin da kwantiraginsa zai kare a Camp Nou.
Kyaftin din Argentina ya yi wa Barcelona wasa 10 a kakar bana, ya kuma ci kwallo shida, har da uku da ya ci a Champions League.
Ranar Alhamis Manchester City ta sanar cewar Pep Guardiola ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu, domin ci gaba da horar da kungiyar.
City tana kishirwar kofin Champions League, saboda haka tana sa ran Guardiola ne zai lashe mata kofin tare da 'yan wasa kamar Lionel Messi.
Barcelona tana mataki na takwas a teburin La Liga da maki 11, za kuma ta fafata a wasan hamayya ranar Asabar inda za ta ziyarci Atletico Madrid a gasar La Liga.
Ita kuwa Manchester City tana ta 10 a kan teburin Premier League da maki 12, za kuma ta ziyarci Tottenham ranar Asabar.