Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Ronaldo, Boateng, Traore, Rice, Janmaat, Upamecano

Asalin hoton, EPA
Manchester United ta tuntubi wakilinCristiano Ronaldo a hukumance a yunkurin dauko dan wasan dan kasar Portugal dagaJuventus. Juve na shirin barin dan wasan mai shekara 35 ya tafi idan ba ta lashe Kofin Zakarun Turai ba. (Record, via Sport Witness)
Arsenal, Chelsea da Tottenham suna son daukar dan wasan Bayern Munich Jerome Boateng. Dan wasan na Jamus, mai shekara 32, zai iya barin kungiyarsa ba tare da ko sisi ba, a yayin da Bayern ta nuna cewa ba za ta sabunta kwangilarsa ba. (Bild, via Sun)
Wolves tana kara jin haushin Adama Traore, wanda har yanzu bai sabunta kwangilarsa ba. Dan wasan na Sifaniya, mai shekara 24, ya amince ya sabunta kwangilarsa da baki ba a rubuce ba a makon jiya. (90min)
Chelsea za ta sake zawarcin dan wasanWest Ham da IngilaDeclan Rice a watan Janairu. Kungiyar za ta sayar da manyan 'yan wasanta biyu domin samun kudin sayen dan wasan mai shekara 28. (Football Insider)
Liverpool na duba yiwuwar daukar dan kasar Netherlands kuma tsohon dan wasan Watford Daryl Janmaat, mai shekara 31, a kwangilar gajeren zango domin magance matsalar da take fama da ita a tsaron gidanta. (Teamtalk)
Kazalika Liverpool na son daukar dan wasan RB Leipzig da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 22, da zummar karfafa tsaron gidanta. (The Athletic - subscription required)
Arsenal ta samu tagomashi a yunkurinta na daukar dan wasan RB Salzburg Dominik Szoboszlai, mai shekara 20, bayan wakilin dan wasan na Hungary ya musanta cewa zai tafi RB Leipzig. (Mirror)
Babu tabbas kan makomar kocinWest Brom Slaven Bilic - a yayin da har yanzu kungiyar ba ta yi nasara a wasan Firimiya na bana ba - kuma an ce kocin Charlton Lee Bowyer na cikin mutanen da ake sa ran za su maye gurbinsa. (Mirror)
Dan wasan Denmark kuma tsohon dan wasan Tottenham Christian Eriksen, mai shekara 28, ya ce halin da yake ciki ba shi ne "abin da ya yi tsammanin fuskanta ba". (TV2, via Goal)
Real Madrid za ta bukaci 'yan wasanta su amince a kara rage alawus-alawus dinsu saboda tasirin da annobar korona. ta yi kan tattalin arzikinta. (ESPN)











