Nigeria Vs Sierra Leone: Karawar shiga gasar kofin Afirka wasa na uku-uku a rukuni

Asalin hoton, The NFF
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta karbi bakuncin ta Saliyo a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za su kara ranar Juma'a.
Wannan ne wasa na uku-uku a cikin rukuni na 12 da tawagogin za su fafata, kuma Super Eagles ce ta daya da maki shida a teburin.
Benin ce ta biyu da maki uku, sai Saliyo ta uku mai maki daya, sanan Lesotho wacce itama keda maki daya tal kuma ta karshe a teburin.
Ranar Asabar 14 ga watan Nuwamba tawagar kwallon kafa ta Benin za ta karbi bakuncin ta Lesotho a daya wasan na rukuni na 12.
Super Eagles za ta ziyarci Saliyo a karawa ta hur-hudu a cikin rukuni ranar 17 ga watan Nuwamba kuma wasa na biyu da za su gwabza.
Da zarar Najeria ta yi nasara a wasannin biyu a jere za ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a 2020.
- 'Yan wasan Super Eagles da aka bai wa goron gayyata:
Masu tsaron raga: Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa); Sebastian Osigwe (FC Lugano, Switzerland); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, Netherlands)
Masu tsaron baya: Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); Chidozie Awaziem (FC Boavista, Portugal); William Ekong (Watford FC, England); Olaoluwa Aina (Fulham FC, England); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany); Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Kevin Akpoguma (TSG 1899 Hoffenheim, Germany)
Masu wasan tsakiya: Oghenekaro Etebo (Galatasaray, Turkey); Tyronne Ebuehi (FC Twente, Netherlands); Frank Onyeka (FC Midtjylland, Denmark); Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland)
Masu cin kwallo: Ahmed Musa (Unattached); Alex Iwobi (Everton FC, England); Emmanuel Dennis Bonaventure (Club Brugge, Belgium); Moses Simon (FC Nantes, France); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Russia)
Masu jiran ko-ta-kwana: Francis Uzoho (APOEL Nicosia, Cyprus); Samson Tijani (TSV Hartberg, Austria); Abdullahi Shehu (Omonia Nicosia, Cyprus); Ramon Azeez (Granada CF, Spain); Kelechi Nwakali (SD Huesca, Spain); Ikechukwu Ezenwa (Heartland FC); Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium)
Wasannin da za a buga ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba:
- Najeriya da Saliyio
- Niger da Ethiopia
- Mali da Namibia
- Morocco da Afirka ta tsakiya
- Afirka ta Kudu da Sao Tome
- Tunisia da Tanzania
Wasannin da za a buga ranar Asabar 14 ga watan Nuwamba:
- Benin da Lesotho
- Jamhuriyar Congo da Angola
- Masar da Togo











