Kasuwar 'yan wasa: Makomar Son, da Pogba, da Ronaldo, da kuma Messi

Tottenham Hotspur ta fara tattaunawa da dan wasa Son Heung-min dan asalin Koriya ta Arewa. Ana sa ran cimma yarjejeniyar ba shi kwantaragi da za ta kai har 2026, inda zai rinka karbar kudi fan 200,000 a kowane mako. (Guardian)

Manchester United na sa ran sayar da dan wasanta na tsakiya Paul Pogba a lokacin musayar 'yan wasa mai zuwa. (Talksport)

Juventus ta bude damar tattaunawa da Paris St-Germain domin musanya dan wasanta dan asalin kasar Portugal Cristiano Ronaldo inda za ta karbi dan asalin Brazil Neymar mai shekara 28 . (Tuttomercato - in Italian)

Sai dai, Ronaldo din a yanzu haka yana duba yiwuwar komawarsaManchester United. (ESPN Argentina, via Metro)

Har yanzu dan wasan tsakiya na Liverpool Georginio Wijnaldum bai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya ba da kungiyar. Kwantaraginsa dai za ta kare za ta kare ne a karshen kakar wasa ta bana. (Liverpool Echo)

Kociyan Barcelona Ronald Koeman ya ce akwai yiwuwar kungiyarsa ta bukaci Wijnaldum a nan gaba. (Sport)

Ana rade-radin cewa Liverpool na son dauko dan wasa David Alaba, sai dai kungiyarsa Bayern Munich ba za ta sayar da shi a cikin watan Janairu mai zuwa ba duk kuwa da cewa yarjejeniyarsa da kungiyar za ta zo karshe ne a shekarar mai kamawa. (Bild - in German)

Burnley defender James Tarkowski says the club's latest contract offer was "nowhere near" good enough. The Englishman, 27, says he has no intention of re-signing with the Clarets

Dan wasan baya na kungiyar Burnley ya ce bai gamsu da tayin sabuwar yarjejeniyar da kulob din ya gabatar masa ba. Ya kuma ce ba ya da aniyar sake sanya hannu kan wata yarjejeniya da kungiyar. (Telegraph - subscription required)

Mahaifin Lionel Messi ya musanta rahotannin da ke cewa dan kwallon zai sauya sheka a kakar wasa mai zuwa daga Barcelona zuwa Paris St-Germain. (Goal)

Arsenal na son dauko dan wasan tsakiya na RB Leipzig Ibrahima Konate da kuma da wasan Faransa Christopher Nkunku. (Bild - in German)