Alex Song: Tsohon dan kwallon Kamaru ya koma Arta Solar 7 ta Djibouti

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan Arsenal da Barcelona, Alex Song ya bayar da mamaki da ya koma Djibouti da taka leda.
Tsohon dan kwallon tawagar Kamaru ya koma wata karamar kungiya Arta Solar 7 da ke Djibouta wacce ba a jin labarinta a fannin tamaula.
''Na saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da Arta. Wannan dama ce don na bunkasa wasannin kwallon kafar Djibouti'', kamar yadda dan wasan ya sanar a twitter.
Dan kwallon mai shekara 33, bai da kwantiragi da kowacce kungiyar tun daga watan Maris, bayan da shi da wasu mutun takwas aka sallamesu daga kungiyar FC Sion ta Swistzerland.
An kori 'yan wasan ne, bayan da suka ki amincewa su rage albashinsu, sakamakon matsin tattalin arziki da kungiyar ta shiga dalilin cutar korona.
Kungiyar ta Arta ta karkare kakar tamaula ta Djibouti a mataki na hudu a teburi a bara, saboda haka za ta wakilci kasar a gasar kofin Afirka ta Confederation.
Arta za ta fara wasan farko na share fage a gasar da kungiyar Masar, Arab Contractors a wasannin cin kofin Afirkan.
Kungiyar ta sanar cewar ranar Alhamis za ta gabatar da Song a gaban magoya bayanta.
An yi mamaki da aka ji Song ya koma Djibouti da taka leda, domin kasarce ta 185 daga 210 a jerin wadanda ke kan gaba a taka leda a duniya a jadawalin Fifa na kwanan nan, kuma ta 51 a Afirka.
Song ya taka leda a Bastia ta Faransa daga nan ya koma Ingila tare da Arsenal, sai ya koma Barcelona kan fam miliyan 20.
Ya buga wasa sama da 100 a Gunners ya kuma lashe kofin La Liga da Barcelona a 2013.
Song ya wakilci tawagar kwallon kafa ta Kamaru Gasar Kofin Duniya da aka yi a Afirka ta Kudu a 2010 da wanda aka yi a Brazil shekara hudu tsakani.











