Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Makomar Eriksen, Bale, Romero, Henderson, Giroud, Dembele

Christian Eriksen playing for Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

An sake ba Tottenham damar sake dauko dan wasan tsakiya na kasar Denmark Christeian Eriksen daga Inter Milan. (Football Insider)

Zai iya yiwuwa kuma Tottenham din ya samu damar dawo da dan wasansa Gareth Bale mai shekara 31 a matsayin kwantaragi na dindindin daga kulob din Real Madrid a farashi mai arha da bai wuce Yuro miliyan 15 ba. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Olivier Giroud na tunanin ci gaba da taka leda a Chelsea, dan wasan wanda a baya aka alakanta shi da yiwuwar zuwa Inter Milan na iya kokarin sauya sheka a kokarin sa na ganin ya kasance cikin tawagar kasarsa ta Faransa a gasar zakarun kasashen nahiyar Turai mai zuwa. (Football London)

Manchester United zai iya gaza dauko Ousmane Dembele a watan Janairu bayan da Barcelona ta nuna alamun ba shi dama a kulob din saboda rashin dan wasanta Ansu Fati wanda ya samu rauni. (Sport - in Spanish)

Yunkurin kulob din Chelsea na dauko tsohon mai tsaron baya na Nottingham Forest Anel Ahmedhodzic daga Malmo na cin karo da matsala, in ji mahaifin dan wasan dan kasar Bosnia. (Sun)

Manchester United na nuna damuwa game da amfani da dan wasan gefe na Ingila Mason Greenwood dan shekara 19 a wurin atisayi. (Times - subscription required)

Manchester United ta dakile yunkurin dan wasa Victor Lindelof dan shekara 26 daga kasancewa tare da tawagar kasarsa ta Sweden a wasan sada zumunta da za su yi da Denmark saboda dokar takaita zirga-zirga da ke aiki yanzu haka a Burtaniya. (Goal)

Manchester United na duba yiwuwar bayar da aron 'yan wasanta uku Ethan Galbraith, da Arnau Puigmal da kuma Ethan Laird a lokacin da za a bude kasuwar musayar 'yan wasa cikin watan Janairu. (Manchester Evening News)

Liverpool ta yi ban kwana da sansaninta na atisayi (Melwood) wanda ta rinka amfani da shi na tsawon shekara 60. (Liverpool Echo)