Ansu Fati: Barcelona za ta yi wata hudu ba tare da dan wasan ba

Asalin hoton, Getty Images
Ansumane Fati zai yi jinyar wata hudu, kafin ya buga wa Barcelona wasanni, bayan da likitoci suka yi masa aiki ranar Litinin.
Matashin dan wasan ya yi rauni ne a karawa da Real Betis a Gasar La Liga, wanda Barcelona ta yi nasara da ci 5-2 a wasannin mako na tara ranar Lahadi.
Ranar Litinin Dakta, Ramon Cugat ya yi masa aikin da aka yi nasara a karkashin kulawar likitocin Barcelona, an kuma tabbatar zai yi jinyar wata hudu.
Matashin dan kwallon ya buga wa Barca wasa 10 da suka hada da bakwai a La Liga da kuma uku a Champions League a shekarar nan.
Haka kuma Fati ya ci kwallo biyar ya kuma bayar da biyu aka zura a raga a kakar bana ta tamaula.
Kawo yanzu matashin ya buga wa Barcelona wasa 43 jumulla, ya kuma ci kwallo 13 ya bayar da uku aka zura a raga.
Cikin kwallayen da ci har da 11 a La Liga da guda biyu a Champions League.
Haka kuma matashin dan wasan ya kafa tarihi da dama tun lokacin da ya fara buga wa Barcelona kwallo.
A dai kakar ta bana, matashin ya buga wa Spaniya wasa hudu a Gasar Nations League da Jamus da Ukraine da Switzerland da kuma Ukraine a karo na biyu.
Kawo yanzu Barcelona tana mataki na takwas a kan teburin La Liga da maki 11.
Wasa biyar da ke gaban Barcelona:
Asabar 21 ga watan Nuwamba La Liga
- Atl Madrid da Barcelona
Talata 24 ga watan Nuwamba Champions League
- Dynamo Kiev da Barcelona
Lahadi 29 ga watan Nuwamba La Liga
- Barcelona da Osasuna
Laraba 2 ga watan Disamba Champions League
- Ferencvaros da Barcelona
Lahadi 6 ga watan Disamba La Liga
- Cadiz da Barcelona











