Valencia ta yi wa Real Madrid ruwan kwallo uku a bugun fenariti

Valencia Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Valencia ta yi nasarar doke Real Madrid da ci 4-1 a wasan mako na tara a Gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi.

Dan wasan Valencia, Carlos Soler ne ya ci kwallo uku rigis a karawar da ta bai wa kungiyar hada maki uku a kan Real Madrid.

Karim Benzema ne ya fara ci wa Real kwallo daga baya Soler ya farke a bugun fenariti aka ce ya sake buga wa ya kuma ci kwallo a karo na biyu.

Dan wasan Real, mai tsaron baya, Raphael Varane ne ya ci gida wasa ya koma ana cin Madrid 2-1, sai Soler ya kara cin kwallo a bugun fenariti, bayan da Mercelo ya yi wa Maxi Gomes keta.

Valencia ta kara cin kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da kyaftin Ramos ya taba kwallo da hannu, kuma Soler ne ya ci fenaritin.

Da wannan sakamakon Real Madrid tana ta hudu a teburin La Liga da maki 16 da kwantan wasa daya da tazarar maki hudu tsakaninta da Real Sociedad mai jan ragamar teburi.

Ita kuwa Valencia tana ta tara da makinta 11, bayan da ta buga wasa tara da fara kakar tamaula ta bana.

Real ta ci karo da cikas, bayan da Bezema ya yi rauni ba a karasa karawar da shi ba, watakila ya shiga jerin wadanda ke jinya a kungiyar.

Soler mai shekara 23, ya zama na uku da ya ci kwallo uku rigis duk da fenariti a wasa daya a Gasar La Liga.