Aston Villa ta ragargaji Arsenal a Emirates a Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Aston Villa da ci 3-0 a wasan mako na takwas a Gasar Premier League da suka fafata a Emirates ranar Lahadi.
Ollie Watkins ne ya ci wa Aston Villa kwallo biyu da hakan ya sa kungiyar ta koma ta shida a kan teburin gasar shekarar nan.
Dan kwallon Arsenal, Bukayo Saka ne ya fara cin gida, bayan da dan wasan Villa, Matt Targett ya buga kwallo zuwa gidan Gunners.
Watkins wanda ya ci Liverpool kwallo uku rigis a wasan da suka yi nasara da ci 7-2, shi ne ya kara na biyu a minti na 72, sannan ya kara na uku minti uku tsakani.
Arsenal ta sa ran yin abin azo a gani a karawar, bayan da ta ci Manchester United 1-0 a wasan mako na bakwai a Old Trafford.
Tun farko sai da Villa ta zura kwallo a ragar Arsenal, amma ba a karba ba, bayan da alkalin wasa ya je ya kalli yadda aka ci kwallon a VAR.
Da wannan sakamakon Arsenal tana nan a matakinta na 11 a kan teburin Premier League, ita kuwa Villa ta ci gaba da buga wasa a waje ba tare da an doke ta ba kawo yanzu a bana.






