Man City 1-1 Liverpool: City tana ta 11 a teburi, Liverpool ce ta uku

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta barar da damar hawa kan teburin Gasar Premier League, bayan da ta tashi 1-1 da Manchester City a Etihad.
Kungiyoyin sun buga karawar mako na takwas a ranar Lahadi, inda Liverpool ta fara cin kwallo ta hannun Mohamed Salah a bugun fenariti.
Liverpool ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga ne, bayan da mai tsaron bayan City, Kyle Walker yayiwa Sadio Mane keta a da'ira ta 18.
City ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Gabriel Jesus, daga nan karawar ta koma 1-1.
Haka kuma Manchester City ta samu damar hada maki uku a wasan , bayan da ta samu fenariti, sai dai kuma De Bryne ne ya buga ta kuma yi fadi ba ta shiga raga ba.
Da wannan sakamakon City tana ta 11 a kan teburi da maki 12, ita kuwa mai rike da kofin bara, Liberpool tana ta uku da maki 17.
Wasannin da kungiyoyin suka fafata a kakar da ta wuce:
Ranar Alhamis 2 ga watan Yuli 2020 Premier League
Man City 4 - 0 Liverpool
10 ga watan Nuwambar 2019 Premier League
- Liverpool 3 - 1 Man City
Lahadi 4 ga watan Agustan 2019 Community Shield
- Liverpool 1 - 1 Man City
A wasa 46 baya da suka kara a Premier League, City ta yi nasara a 10, Liverpool ta ci 20 da canjaras 16.
Shin ko kun san?
Manchester City ta ci wasa uku baya a Etihad a karawa da Liverpool da kwallo 11-1.
Sai dai kuma City ba ta taba doke Liverpool a gida sau hudu a jere ba tun bayan watan Maris din 1937.
Pep Guardiola ya sha kashi a hannun kocin Liverpool, Jurgen Klopp sau takwas fiye da kowanne a tarihinsa na horar da tamaula.
Liverpool na fatan buga wasa a karon farko ba tare da an zura mata kwallo ba a Etihad a fafatawa ta 11.
A tsawon wannan lokacin an zura mata kwallo 26 a kaarawa 10 baya da cin wasa daya da canjaras biyu da shan kashi bakwai.
Diogo Jota na Liverpool ya ci kwallo uku a wasan da yake shiga daga baya a Premier League, babu wanda ya yi wannan bajintar fiye da shi a kakar bana.
Wadanda suka alkalanci karawar:
Alkalin wasa: Craig Pawson
Mataimakansa: Lee Betts da kuma Richard West
Mai jitan ko-ta-kwana: Andre Marriner
Mai kula da VAR: Paul Tierney
Mataimakinsa:Stephen Child.
Sakamakon wasannin da aka buga a Gasar Premier League karawar mako na takwas:
Juma'a 6 ga watan Nuwamba
- Brighton & Hove Albion 0-0 Burnley
- Southampton 2-0 Newcastle United
Asabar 7 ga watan Nuwamba
- Everton 1-3 Manchester United
- Crystal Palace 4-1 Leeds United
- Chelsea 4-1 Sheffield United
- West Ham United 1-0 Fulham
Lahadi 8 ga watan Nuwamba
- West Bromwich Albion 0-1 Tottenham
- Leicester City 1-0 Wolverhampton Wanderers










