EndSARS: Abin da Ƴan kwallon Najeriya suka ce kan zanga-zangar EndSARS

Lokacin karatu: Minti 3

'Yan wasan kwallon kafa na tawagar Najeriya da dama sun yi tsokaci kan zanga-zangar EndSARS da ta rikiɗe ta koma rikici a Najeriya.

Yawancin ƴan ƙwallon sun yi roƙon yi wa Najeriya addu'a ne kan halin da ta shiga bayan zargin sojoji da bude wa masu zanga-zanga wuta a Legas, zargin da rundunar sojin Najeriya ta musanta.

A ranar Talata ne gwamnatin Legas ta sanya dokar hana fita ta sa'a 24, bayan zanga-zangar da aka fara ta lumana ta rikiɗe ta koma rikici.

Ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ba a ranar Talata a Legas, amma ƙungiyar Amnesty Interntional a Najeriya ta ce tana da sahihan shaidu masu tayar da hankali da suka tabbatar da an yi amfani da ƙarfi da suka haddasa kashe-kashen.

Masu zanga-zangar sun bijere wa dokar hana fita da gwamnati ta sanya wacce ta fara aiki tun ƙarfe huɗu na yammacin Talata.

Abin da ƴan ƙwallon suka ce

'Yan kwallon na Najeriya sun yi tsokaci ne a shafukansu na Twitter.

Kaftin ɗin Super Eagle Ahmed Musa, ya yi jaje ga waɗanda suka rasa rayukansu ga abin da ya kira kisan gillar da ta faru ranar Talata. "Abin takaici ne cewa mun rasa ƴancin yin zanga-zangar lumana. Ya kamata gwamnati ta yi abin da ya dace domin kawo ƙarshen wannan kariyar zuciya."

Tsohon kaftin din Super Eagles yana cikin waɗanda suka yi kiran dakatar da kashe masu zanga-zangar, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter ɗauke da maudu'in EndSARS inda ya ce "a yi wa Najeriya addu'a da dakatar kisa."

Dan wasan Super Eagles na Manchester United Odion Jude Ighalo shi ma ya yaɗa bidiyo a shafinsa na Twitter inda ya kira abin ke faruwa a Najeriya a matsayin wani abin baƙin ciki. A cikin kalamansa, Ighalo ya soki gwmanatin Najeriya inda ya ce "gwamnati ta kunyata ƴan Najeriya a idon duniya. Ya kuma yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da gwamnatin Birtaniya su ɗauki mataki kan abin da ke faruwa a Najeriya."

Victor Osimhen, wanda ke taka leda a Napoli ta Italiya ya nemi kawo karshen kashe-kashe, inda ya daga farar riga a wasan da kungiyar ta buga. Sakon na cewar ''A kawo karshen kashe-kashen da 'Yan Sanda ke yi a Nijeriya.

Victor Moses ya wallafa saƙo ɗauke da maudu'in EndSARS da kuma hoton tutar Najeriya.

Tsohon dan kwallon Arsenal, Alex Iwobi shi kuwa kira ya yi da a kare rayuka ba wai salwantar da su ba.

Asisat Oshoala yar wasan tawagar Najeriya mai taka leda a Barcelona tun a baya ta bayyana goyon bayanta da cewar ''Da jikin mu suke samun yin mulki''

Shi kuwa Troost Ekong ya bayar da shawara kan abu biyar da gwamnatin Muhammadu Buhari ya kamata ta yi ta kawo karshen zanga-zanga ta EndSARS