Real Madrid vs Shakhtar Donetsk: Real ta yi rashin nasara a wasa uku a jere a Gasar Zakarun Turai

Mai rike da kofin Champions League 13, Real Madrid ta fara kakar bana da kafar hagu, bayan da Shakhtar Donetsk ta yi nasara a kanta da ci 3-2 a Spaniya.

Kungiyar ta Ukraine ta je Madrid ba tare da manyan 'yan wasanta 13 ba, bayan da daukacinsu suka kamu da cutar korona, hakan ne ya sa ta ziyarci Spaniya da matasanta.

Kungiyar da Luis Castro ya ja ragama ta fara cin kwallo 3-0 tun kan hutu a filin wasa na Alfredo di Stefano wanda ya karbi bakuncin gasar a karon farko, sai dai ba 'yan kallo saboda gudun yada cutar korona.

Bayan da suka koma karawar zagaye na biyu ne Luka Modric da kuma Vinicius Junior suka zare kwallo biyu da hakan ya kara mata kwarin gwiwa.

Federico Valverde ne ya ci wa Real kwallo na uku daf da za a tashi, amma da aka duba VAR, sai alkalin wasa, Srdjan Jovanovic ya soke kwallon da cewar an yi satar gida.

Wannan ne kano na uku da kungiyoyin suka fafata a Gasar ta Zakarun Turai ta Champions League.

Sun fara karawa ranar 15 ga watan Satumbar 2015, inda Real ta yi nasara da ci 4-0.

A wasa na biyu kuwa Shakhtar ta yi rashin nasara a gida da ci 4-3.

'Yan kwallo 19 da Zinedine Zidane ya fuskanci Shakhtar Donetsk a Spaniya

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Militao da Varane da Nacho da Marcelo da kuma Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modrić da Casemiro da Valverde da kuma Isco.

Masu cin kwallo: Benzema da Asensio da Lucas V da Jovic da Vini Jr. da kuma Rodrygo.

Real Madrid ta karbi bakuncin Shakhtar Donetsk a Champions League a kaka ta 51 da take buga a gasar.

Kakar Gasar Champions League ta 2020-21 ita ce ta 66 da zakarun kungiyoyin nahiyar Turai kan kara a tsakaninsu da hukumar kwallon kafa ta Turai kan shirya.

Kuma ita ce ta 29 tun bayan da aka sauya mata fasali daga European Champion Clubs Cup zuwa UEFA Champions League.

Real ita ce kan gaba wajen halartar wasannin, kuma a karon farko za ta buga fafatawar bana a filinta da take atisaye mai suna Alfredo Di Stefano.

Wannan ne wasan farko da filin zai karbi bakuncin Gasar Champions League, bayan karawa biyar a Gasar La Liga da wasa biyu da tawagar kwallon kafa ta Spaniya ta taka rawa a filin a shekarar nan.

Babu wata kungiya da ta kai Real Madrid zuwa Gasar Champions League, ta kuma lashe kofin sau 13 tun da aka fara wasannin a 1955.

Kungiyar Benfica ce kusa da Real Madrid a yawan zuwa gasar da ta yi 39, sai Bayern Munich da Ajax da kuma Dynamo Kiev da kowacce ta buga 36.

Abubuwa na bajinta da aka yi a karawar:

  • Real Madrid ta yi rashin nasara a gasar Zakarun Turai karo uku a jere a karon farko tun bayan Satumbar 1986. A bara ne Manchester City ta doke Real a Spaniya da kuma Ingila a gasar ta Champions League
  • Shakhtar ce ta farko daga Ukraine da ta yi nasara a kan Real a Champions League tun bayan Maris din 1999, lokacin da Dynamo Kiev ta ci 2-0.
  • Raphael Varane ya zama dan wasan Real na uku da ya ci gida kwallo biyu a Champions League, bayan Ivan Helguera and Sergio Ramos.
  • Vinicius Junior ya ci wa Real kwallo dakika 15 da shiga fili, bayan da ya canji dan wasa - shi ne na farko da ya yi wannan a Champions League tun 2006-07 (Lokacin da Opta ta fara tara bayanai).
  • Luka Modric ya zama dan wasa na hudu da ya ci wa Real kwallo a Gasar European Cup/Champions League yana da shekara 35, bayan Alfredo Di Stefano da Ferenc Puskas da kuma Paco Gento.
  • Golan Shakhtar, Anatolii Trubin ya zama matashi na biyu da ya kara da Real a tarihin Champions League (shekara 19 da kwana 81), wanda ya fara shi ne Timon Wellenreuther na Schalke a Fabrairun 2015, yana da shekara 19 da kwana 77.

Karo na biyu a jere da Madrid ta yi rashin nasara a bana, bayan da Cadiz ta doke ta a Gasar La Liga 1-0 ranar 17 ga watan Oktoba.

Ranar Asabar Real za ta ziyarci Barcelona domin karawa a gasar La Liga wasan hamayya na El Clasico na farko a bana.