Kano Pillars: Kungiyar ta dauki bature Lione Emmanuel matsayin sabon kocinta

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Kungiyar Kano Pillars ta dauki sabon koci, Lione Emmanuel Soccia kan yarjejeniyar shekarar daya, in ji shugaban kungiyar Surajo Shu'aibu Yahaya.

Kano Pillars za ta wakilci Nigeria a gasar cin kofin Afirka na Confederation Cup a kakar bana ta 2020-21.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf ce ta umarci dukkan kungiyoyin da ke cikin gasar Afirka ta bana da su tabbatar kocinsu yana da lasisin horar da tamaula mai matakin ''A''.

Lione Emmanuel ya yi takara da mutum takwas inda biyar daga kasashen waje da masu horar da kwallon kafa daga gida Najeriya.

Surajo Shu'aibu ya ce dalilin da ya sa suka zabi kocin ''Ya cika dukkan ka'idar da hukumar kwallon Afirka ta gindaya, domin yana da lasisin horar da kwallo a Turai wato UEFA matakin ''A'' da na Afirka da aka bukata.''

''Haka kuma ya horar da tamaula a kasashen Afirka da suka hada da Kamaru da Gabon da Tanzaniya da kuma Afirka ta Kudu. ''Ya kuma samu nasara da yawa a gasar kwallon kafar Afirka.''

Pillars na fatan kocin ya kai ta matakin karawar cikin rukuni, bayan kammala fafatawar sharan fage a kakar shekarar nan.

Shugaban na Pillars ya ce za su bai wa kocin Albashin naira miliyan 1,7000, kuma Lione Emmanuel ne da kansa ya fayyace cewar yana da sha'awar koci a Najeriya a kungiya ta Enyimba ko Rangers ko kuma Kano Pillars.

Haka kuma Pillars din ta nada Ibrahim Musa da ake kira Jugunu a matakin wanda zai taimaka wa sabon kocin dan kasar Faransa gudanar da aiki.

Kano Pillars ta kasa kai wa zagayen gaba a gasar Confederation ta bara, bayan da Asante Kotoko ta Ghana ta yi nasara a kanta.

A wasan farko da suka buga a Sani Abacha, Pillars ce ta yi nasara da ci 3-2 ranar 10 ga watan Agustan 2019, a Ghana kuwa Asante ce ta ci 2-0 ranar 25 ga watan Agustan 2019.

Pillars wacce ta lashe kofin Najeriya karo hudu ta samu wakiltar kasar a gasar Zakarun Afirka ta bana, bayan da ta lashe kofin kalubalen kasar a bara, amma cutar korona ta hana wasanni a bana, da hakan ya sa aka bai wa kungiyar ta Kano gurbin.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta karkare kakar bara ta ayyana Plateau United a matakin wacce ta lashe kofin, sakamakon bullar cutar korona da ta sa aka dakatar da dukkan wasanni a fadin duniya.

Wannan ne karo na biyu da Shugaban Pillars da ake yi wa lakabi da John Bull zai ja ragamar kungiyar kaka ta biyu a Gasar cin kofin Nahiyar Afirka.