Barcelona: Messi ya ci kwallo a karawar da ta doke Ferencvarosi 5-1 ranar Talata

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Lionel Messi yana daga cikin 'yan kwallon Barcelona da suka doke Ferencvarosi da ci 5-1 a Gasar Champions League ranar Talata.

Lionel Messi ne ya fara cin kwallo a bugun fenariti minti na 27 da fara wasan, sannan Ansu Fati ya kara na biyu kan su je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Barcelona ta kara na uku ta hannun Philippe Coutinho sai Pedri ya kara na hudu, sannan Ousmane Dembele ya cike na biyar.

Ita kuwa Ferencvarosi ta ci kwallonta a bugun fenariti saura minti 20 a tashi daga wasan ta hannun Ihor Kharatin.

Kwallon da Messi, kyaftin din tawagar Argentina ya ci ya zama saura 14 ya tarar da Cristiano Ronaldo wanda ke kan gaba da 130 a gasar ta Champions League.

Juventus wacce take rukuni daya da Barcelona ta yi nasara ne da ci 2-0 a gidan Dynamo Kiev.

Da wannan sakamakon Barcelona tana ta daya a rukuni na bakwai, sai Juventus ta biyu, sannan Dynamo Kiev, sai Ferencvarosi ta hudu ta karshe.

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid ranar Asabar 24 ga watan Oktoba a karawar da ake kira ta El Clasico ta farko a bana a Gasar La Liga.