Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Ozil, De Bruyne, Upamecano, Sarri, Bale, Cuisance

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal tana son sake tattaunawa da dan wasan Jamus Mesut Ozil, mai shekara 31, a game da yiwuwar kawo karshen kwangilarsa kafin a bude kasuwar 'yan kwallo ta watan Janairu. (Mail)
Manchester City na samun ci gaba a kan yarjejeniyar da za ta kulla da dan wasan tsakiyar Belgium Kevin de Bruyne. Tana son dan wasan mai shekara 29 ya sanya hannu kan kwangilar shekara biyar. (Times)
Manchester United za ta yi yunkurin daukar dan wasan RB Leipzig da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 21, a kan £36.5m a bazara mai zuwa. Liverpool da Manchester City suna son daukar dan wasan. (Bild, via Sun)
Tsohon dan wasanManchester United Memphis Depay, mai shekara 26 dan kasar Netherlands wanda yanzu yake murza leda a Lyon, ya ce "wasu ka'idoji" ne suka hana shi tafiya Barcelona lokacin musayar 'yan kwallon da ya wuce. (AS)
Tsohon kocin Chelsea da Juventus Maurizio Sarri yana son zama kocin Fiorentina. (Tuttomercato - in Italian)
Dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 31, yana son lashe gasar Firimiya ta bana tare da Tottenham, a cewar manajansa. (Sky Sports)
Dan wasan tsakiyar Faransa Michael Cuisance, mai shekara 21, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa rashin nasara kan gwajin lafiyarsa ne dalilin da ya sa bai tafi Leeds ba. Daga bisani ya tafi Marseille domin yin zaman aro daga Bayern Munich. (Sky Sports)
Liverpool za ta tattauna da Harry Wilson a kan yiwuwar bayar da aronsa da zarar dan wasan mai shekara 23 ya koma daga Wales inda yake wasannin duniya. (Standard)
Bournemouth ba za ta bari dan wasan tsakiyar Wales David Brooks ya tafi ba kafin a kammala musayar 'yan kwallo ta Ingila. Sheffield United na son dan wasan mai shekara 23. (Football Insider)
West Ham na duba yiwuwar mika £5m don dauko dan wasan QPR dan kasar Ireland Ryan Manning.
Manchester United ta yi watsi da bukatarPenarol ta daukar aron dan wasan Uruguay Facundo Pellistri, mai shekara 18 nan take har sai bayan watan Janairu. (Manchester Evening News)











