Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Dembele, Sarr, Rose, Anderson, Romero, Knockaert

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasanBarcelona dan kasar Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, bai nuna sha'awar tafiya Manchester United kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo ba amma yana son tafiya Juventus a bazara mai zuwa. (Catalunya Radio, via Mirror)
Manchester United ba za ta yi zawarcin dan wasan Watford dan kasar Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 22 ba, kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo ta EFL ranar 16 ga watan Oktoba. (Goal)
KocinTottenham Jose Mourinho zai cire dan wasan Ingila Danny Rose, mai shekara 30, daga tawagar da ya yi wa kwaskwarima mai kunshe da 'yan wasa 25, wadda za a kammala hadawa ranar 20 ga watan Oktoba. (Mail)
Dan wasanWest Ham da Brazil Felipe Anderson ya ce yana "cika burinsa" na murza leda a kungiyar da ke buga Gasar Zakarun Turai bayan ya tafi zaman aro na kakar wasa daya a Porto sai dai ya ce ya yi amanna zai koma West Ham.(Talksport)
West Ham na son dauko dan wasan baya daga Turai a yayin da suke neman dan wasan tsakiya da zai maye gurbin Anderson. (London Evening Standard)
GolanManchester United dan kasar Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, yana son tafiya Amurka ko Canada don murza leda bayan da ya kasa tafiya Everton har aka rufe kasuwar 'yan kwallo. (Mail)
Sabon kocin Nottingham Forest Chris Hughton yana son karbo aron dan wasan Fulham Anthony Knockaert, mai shekara 28. (Sky Sports)
Dan wasanAston Villa Jack Grealish, mai shekara 25, ya bayyana yadda ya kwashe mako uku yana jan hankalin dan wasan Ingila Ross Barkley, mai shekara 26 domin ya tafi wurinsu daga Chelsea. (London Evening Standard)
Grealish na cikin 'yan wasa hudu da Ole Gunnar Solskjaer ya so amma Manchester United ba ta dauke shi ba kafin rufe kasuwar 'yan kwallo. (ESPN)
Dan wasan daManchester United ta dauko dan kasar Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, ya bayyana cewa zai tafi kungiyar kwallon kafar Argentina Boca Juniors idan ya kammala zamansa a Old Trafford. (Goal)
Cavani ya bayyana cewa ya kusa yin ritaya daga kwallon kafa bayan budurwarsa ta kamu da Covid-19. (Manchester Evening News)
Dan wasan Croatia Luka Modric, mai shekara 35, zai ci gaba da zama a Real Madrid kuma zai amince a rage albashinsa a kungiyar. (Marca)











