Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Sancho, Tomori, Rodon, Wijnaldum, Garcia, Depay

Fikayo Tomori

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta janye jikinta daga cinikin dan wasan Ingila Jadon Sancho, 20, bayan ta gano cewa daukarsa za ta sa ta biya kusan £227m saboda kudin tayin sayensa £108m, da alawus-alawus da kuma kudin da wakilin dan wasan na Borussia Dortmund yake so a biya shi. (Guardian)

West Ham ta matsu sosai a yunkurin da ta yi na karbar aron dan wasan Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 22, abin da ya sa ta so bai wa Chelsea £50,000 a duk lokacin da bai buga wa Hammers ba, amma duk da haka cinikin bai fada ba. (Talksport)

Tottenham da West Ham na son dan wasan Swansea dan yankin Wales Joe Rodon, mai shekara 22, kuma za ta iya biyan £18m kafin karshen wa'adin rufe kasuwar EFL ranar 16 ga watan Oktoba. (Wales Online)

West Ham za ta iya yunkurin dauko dan wasan Watford dan kasar Ingila Craig Dawson, mai shekara 30, amma akwai bukatar ta biya £4m. (Sun)

Watfordta yi watsi da tayin daManchester United ta yi na daukar dan wasan Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 22 don ya yi zaman kakar wasa daya, amma za ta iya sake gwada daukarsa a wannan watan, ko da yake Hornets na so ya tafi dindindin. (Manchester Evening News)

Dan wasanLiverpool dan kasar Netherlands Georginio Wijnaldum ya yi watsi da rade radin da ake yi cewa Barcelonatana zawarcinsa. Kwangilar dan wasan mai shekara 29 za ta kare a Anfield a bazara mai zuwa. (Mirror)

Kungiyar Saint-Etienne ta Faransa ta soki Arsenal saboda gazawarta wajen hukunta dan wasan Faransa mai shekara 19 William Saliba kan komawarsa kungiyar. (Talksport)

Barcelona za ta jira sai bazarar 2021 domin dauko dan wasan Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, daga Manchester City. (Marca)

Yunkurin Barcelona na dauko dan wasan Lyon da Netherlands Memphis Depay, mai shekara 26, ya fuskanci matsala daga dan wurin wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, saboda ya ki tafiya Manchester United. (AS)

Watford da Middlesbrough suna son aron dan wasan Chelsea da Ghana Baba Rahman, mai shekara 26, domin yin zaman kakar wasa daya. (Goal)