Gunnersaurus: Mesut Ozil ya yi tayin biyan albashin mutum mutumin Gunners

Dan kwallon Arsenal, Mesut Ozil ya yi tayin zai biya albashin Jerry Quy, mai shigar mutum mutumin Gunners da ake kira Gunnersaurus.

Ranar Litinin Gunners ta sanar cewar Quy wanda shi ne ke shigar mutum mutumin Arsenal shekara 27 yana cikin mutum 55 da aka kora daga aiki a kungiyar.

“Na ji bakin ciki da Jerry Quy, wanda aka fi sani da sunan Gunnersaurus wanda ke kashin bayan kungiyarmu cewar an sallame shi, bayan shekara 27 yana aiki,” in ji dan kasar Jamus kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a Twitter.

“Saboda haka ina yi masa tayin biyansa albashi da Arsenal ke ba shi, saboda Jerry ya ci gaba da gudanar da aikin da yake kauna matuka.”

Arsenal ta fada cewar ya zama wajibi ta rage ma'aikatanta, saboda tabarbarewar tattalin arziki da cutar korona ta hadasa.

'Yan wasan Gunners da koci Mikel Arteta sai da suka rage albashi kaso 12.5 cikin 100 a watan Afirilu.

Su ma jami'an kungiyar sai da suka zabtare swani kaso na albashinsu zuwa shekara daya.

Sakamakon bullar annobar tun cikin watan Maris ta sa ana buga gasar Premier League ba tare da 'yan kallo ba.