Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Pochettino, Garcia, Shaqiri, Stones, Anderson, Dawson
Manyan jami'an Manchester United sun tuntubi wakilan Mauricio Pochettino domin daukarsa idan suka kori Ole Gunnar Solskjaer. (Star)
Manchester City ta ki amincewa da tayin Barcelona na £15.4m da kuma kudin tsarabe-tsarabe kan dan wasan Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, a ranar rufe kasuwar 'yan kwallo. (Sky Sports)
Dan wasan Liverpool dan kasar Switzerland Xherdan Shaqiri, mai shekara 28, ya yi kwantai domin kuwa babu kungiyar da ta nemi daukarsa a lokacin musayar 'yan kwallo, don haka ana sa ran zai ci gaba da zama har watan Janairu tun da kungiyar ba za ta bayar da aronsa ba. (Goal)
Dan wasanManchester City da Ingila John Stones, mai shekara 26, ya ki amincewa ya tafi zaman aro Tottenham saboda ba ya son ya bar iyalinsa a baya. (Star)
Porto na son karbar aron dan wasan West Ham da Brazil Felipe Anderson, mai shekara 27, zuwa karshen kakar wasa. (Sky Sports)
West Ham tana tattaunawa domin dauko dan wasan Ingila mai shekara 30 Craig Dawson daga Watford. (Football Insider)
Barcelona ta yi asarar kudin shiga fiye da euro 200m (£181m) sakamakon annobar korona. (Telegraph)
Kocin Paris St-Germain Thomas Tuchel bai ji dadin matakin da kungiyar ta dauka na kin sayo dan wasa a kasuwar musayar 'yan kwallo ba. (Guardian)