Karim Benzema: Shi ne ya ci na biyu kuma na farko a bana a wasa da Levante

Asalin hoton, Getty Images
Mai rike da kofin La Liga, Real Madrid ta ci gaba da lashe wasanninta, bayan da Vinicius Junior da Karim Benzema suka samar mata maki uku a gidan Levante.
Kawo yanzu dan wasan tawagar Brazil, Vinicius ya ci wa Madrid kwallo a wasa biyu a jere a La Liga a karon farko.
Daga nan ne Benzema ya ci na biyu daf da za a tashi kuma na farko a kakar bana ta 2020-21.
Vinicius shi ne ya ci wa Madrid kwallon da ta yi nasara a gida da Valladolid ranar 30 ga watan Satumba.
Bayan yin nasara a wasa uku a jere, Real Madrid ta dare mataki na daya a teburin La Liga na shekarar nan.
Dan wasan tawagar Faransa bai ci wa Real kwallo ba a karawar da ta yi da Sociedad da Real Betis da Real Valladolid a farkon kakar bana ba.
Benzema shi ne na biyu a yawan cin kwallaye a raga a bara, bayan 21 da ya ci daga 70 da Real wacce ta dauki kofin La Liga.
Dan kwallon Barcelona, Lionel Messi shi ne ya lashe takalmin zinare a gasar La Liga da ta wuce, wanda ya ci 25 daga 86 da kungiyar ta zura a raga.











