Atletico Madrid: Luis Suarez ya ƙulla yarjejeniyar shekara biyu da ƙungiyar

Luis Suarez signing his contract to join Atletico Madrid

Asalin hoton, Twitter:@Atleti

Bayanan hoto, Luis Suarez ya lashe Kofin La Liga hudu a Barcelona

Atletico Madrid ta kammala sayen dan wasan gaba Luis Suarez daga abokiyar hamayyarta a La Liga Barcelona.

Dan wasan na Uruguay ya sanya annu kan yarjejeniyar shekara biyu da kungiyar ranar Juma'a bayan ya an gama duba lafiyarsa.

Dan wasan mai shekara 33 ya je Barca daga Liverpool a 2014, inda ya ci kofin Zakarun Turai a kakarsa ta farko a Sufaniya.

Kazalika Suarez ya taimaka wa Barca wajen lashe Kofuna hudu, inda ya ci kwallo 198 a wasanni 283 da ya murza wa kungiyar.

Atleti ta biya euro 6m kan dan wasan, wanda si ne dan wasa na uku da ya fi zura kwallo a tarihin Barcelona.

Barca ta sayi suarez a kan £74m daga Liverpool amma sabon kocinta Ronald Koeman ya shaida wa dan kasar ta Uruguay a watan jiya cewa ba ya son yin aiki tare da shi.

Tsohon dan wasan na Ajax ya amince ya tafi Juventus amma ya gaza komawa can saboda bai samu fasfon Italiya ba.

Suarez ya zubar da hawaye ranar Alhamis a yayin da yake bankwana da Barcelona.

Lionel Messi ya ce Luis Suarez ya cancanci a yi masa karramawar da ta fi wadda Barcelona ta yi masa da zai bar kungiyar kodayake ya ce a halin yanzu "babu abin da yake ba ni mamaki" kan abin da aka yi wa dan wasan.