Lionel Messi ya ce bai ji daɗin wulaƙancin da Barcelona ta yi wa Luiz Suarez ba

Lionel Messi and Luis Suarez high five

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Suarez ya bar Barcelona bayan shekara shida

Lionel Messi ya ce Luis Suarez ya cancanci a yi masa karramawar da ta fi wadda Barcelona ta yi masa da zai bar kungiyar kodayake ya ce a halin yanzu "babu abin da yake ba ni mamaki" kan abin da aka yi wa dan wasan.

Suarez ya tafi Atletico Madrid bayan sabon kocin Barca Ronald Koeman ya ce ba shi da niyyar yin aiki tare da shi.

Ya kara da cewa yana ganin shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya yaudare shi.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Messi ya jinjina wa Suarez, yana mai cewa zai zama "bambarakwai" a gan shi "sanye da wata rigar kwallo" da ba ta Barcelona ba ko ma su fafata a wasa daga kungiyoyi daban-daban.

"Ka cancanci a yi maka karramawar da ta dace da matsayinka - kai ne daya daga cikin 'yan kwallon kafa mafiya muhimmanci a tarihin kungiyar, ka yi nasarar samun muhimman abubuwa da dama a kungiyance da kuma kai kadai.

"Bai kamata a yi maka wulakancin da aka yi maka ba. Sai dai a halin da ake ciki babu abin da yake ba ni mamaki."

Dan wasan Uruguay Suarez ya zura kwallo 198 a wasanni 283 da ya buga mata inda ya zama dan wasa na uku da ya fi zura kwallo a tarihin Barcelona.

Suarez mai shekara 33 ya lashe Kofin La Liga hudu, Copa del Reys hudu, Kofin Zakarun Turai daya, Kofin Duniya na nahiyoyi da ake kira Club World Cup a 2015 tun da kungiyar ta saye shi daga Liverpool a shekarar 2014 a kan £74m.