Cristiano Ronaldo ya zura kwallo fiye da 100 a wasan da ya buga wa Portugal

Asalin hoton, EPA
Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo ya zama dan kasar Turai na farko da ya zura kwallo 100 a wasan da aka fafata da wata kasa rukunin kwallon kafar maza kuma ya zarta wannan adadi bayan ya ci kwallo biyu a gasar Nations League inda suka yi nasara a kan Sweden.
Kyafin din ya cilla wata kwallo da suka samu bugun firi kik - wanda shi ne na 57 da ya buga a tarihin kwallon kafarsa- inda ya jefa ta a raga.
Dan wasan gaban na Juventus, mai shekara 35, ya zura kwallonsa ta biyu daga wajen da'ira kuma hakan na nufin ya ci kwallo 101 a wasa 165 da ya buga wa kasarsa.

Ronaldo, wanda ya buga wasa na minti 81, yana da sauran kwallo takwas da zai ci don kafa tarihi.
Dan wasan Iran Ali Daei - wanda shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar kasashen duniya fiye da Ronaldo - ya ci kwallaye 109 lokacin da yake ganiyarsa daga 1993 zuwa 2006.
Sauran 'yan kwallon da ke wannan rukuni su ne dan wasan India Sunil Chhetri (72) da dan wasan Argentina Lionel Messi (70).
Sakamakon wasan na nufin kasar Portugal da ke kare kambunta na gasar Nations League ta ci wasanninta biyu na farko a gasar ta wannan shekarar.







