Cristiano Ronaldo ya zama biloniya

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo ya kasance dan wasan kwallon kafa na farko a tarihi da ya samu fiye da dala biliyan daya kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.
Dan wasan Juventus din ya samu dala miliyan 650 a buga kwallon kafa, sannan ya samu sauran kudin wajen tallar hajoji.
Ronaldo ya zama dan wasa na uku da ya kai wannan matakin, inda ya shiga rukuninsu dan wasan Golf, Tiger Woods da kuma dan dambe Floyd Mayweather.
Ronaldo ya samu dala miliyan 105 a bara kuma dan wasan Tennis Roger Federer ne kawai ya shiga gabansa a samun kudi cikin 'yan wasa a bara.
Dan wasan ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau biyar sannan ya murza leda a Manchester United da Real Madrid kafin ya koma Juventus.
Ana sa ran babban abokin hammayarsa Lionel Messi ya shiga wannan rukunin na wadanda suka samu fiye da dala biliyan daya a shekara mai zuwa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X






