Cristiano Ronaldo ya yi iya abin da zai iya a Champions League - 'Yar uwarsa Elma

Asalin hoton, Elma
'Yar uwar Cristiano Ronaldo ta yi ƙoƙarin lallaɓa magoya bayan ƙungiyar Juventus bayan tauraron ɗan uwan nata ya gaza taimaka wa ƙuniyar shiga zagayen gaba a gasar Champions League a daren jiya.
Zakarun na Italiya sun yi waje daga gasar ne duk da cewa Ronaldo ne da kansa ya ci mata ƙwallo biyun da ta doke Lyon da 2-1.
Sai dai Lyon ce ta fara cinye Juve a Faransa 1-0 a wasan farko na watan Maris.
Tun a minti na 12 Memphis Depay ya ci wa Lyon bugun finareti kafin Ronaldo ya ci nasa finaretin a minti na 43 sannan ya ƙara ta biyu daga wajen yadi na 18 a minti na 60.
Tun bayan da ya koma Juve daga Real Madrid shekara biyu da suka wuce, Ronaldo ne ya ci ƙwallo duka bakwai da Juve ta ci a zagayen 'yan 16 na Champions League.
'Yar uwarsa mai suna Elma ta ce ɗan uwanta na buƙatar ƙarin goyon baya da tallafi daga abokan wasansa idan har suna so ya sake lashe kofin a karo na shida.
"Ka fi sauran ƙoƙari ɗan uwana. Ian alfaharin ganinka kana taka leda da kuma jajircerwarka, amma duk da haka ba za ka iya yin komai kai kaɗai ba," Elma ta wallafa a shafinta na Instagram.
"Ka san haka ƙallo take, ya kamata ka tuna cewa ka yi iya abin da za ka iya kuma har yanzu kai ne gwarzo a duniya."
A daren Juma'ar dai Manchester City ta yi wajerod da Real Madrid daga gasar bayan ta lallasa ta 2-1 har sau biyu, wasa gida da waje.
Yanzu Lyon za ta kara da Man City a zagayen kwata fayinal, inda wannan karon wasa ɗaya kawai za a buga - ba gida da waje ba kamar yadda aka saba.
Za a buga wasannin ne baki ɗayansu a birnin Lisbon na Portugal.











