Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Koulibaly, Werner, Depay, Fraser, Tarkowski, Benrahma

Shugaban Napoli Aurelio de Laurentiis ya ce dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, zai bar kungiyar idan aka yi musu tayi mai armashi a bazara kuma Manchester United da Manchester City su ne kan gaba a yunkurin dauko dan wasan. (Talksport)

City za ta sake taya Koulibaly a kan £66m a makon gobe. (Inside Futbol)

Sabon dan wasan Chelsea Timo Werner, mai shekara 24, ya yi watsi da damar tafiya Manchester City bayan Pep Guardiola ya kira shi domin tattaunawa kan yiwuwar tafiyarsa kungiyar. (Mail)

West Ham ta mika fiye da £20m don dauko dan wasan Burnleydan kasar Ingila James Tarkowski, mai shekara 27. (Sky Sports)

Barcelona ta amince ta dauko dan wasan Netherlands Memphis Depay, mai shekara 26, daga Lyon. (Teamtalk)

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya janye kalaman da ya yi cewa ba zai taba zama kocin Barcelona saboda alakarsa da abokan hamayyarta Espanyol. (Sun)

Manchester United na shirin janyewa da yunkurinta na dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho saboda suna ganin farashin da aka sanya wa dan wasan ya yi matukar yawa. (Star)

Barcelonata ki amincewa da tayin da Tottenhamta yi mata na sayen dan wasan tsakiya Lucas de Vega. Ko da yake De Vega yana son barin kungiyar, amma Barca tana so ta saka shi a rukuninta na biyu a kakar wasa mai zuwa (Sport - in Spanish)

Barcelona tana da kwarin gwiwar cewaza ta iya dauko dan wasan Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 29, daga Liverpool. (Goal)