Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi: Ɗan wasan Barcelona ya fasa barin ƙungiyar
Shahararren ɗan ƙwallon ƙafar nan ɗan Barcelona, Lionel Messi, ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a Barcelona, sakamakon ba zai yiwu wata ƙungiya ta iya biyan farashin da Barcelona take nema a kansa ba.
Lionel Messi, wanda shi ne ɗan wasan da ya fi cin ƙwallaye a tarihin ƙungiyar, ya ce zai haƙura ya ci gaba da zama a Barcelona sakamakon bai so ya kai kulob ɗin da yake so ƙara a kotu.
Ɗan wasan wanda ɗan asalin Argentina ne a Talatar da ta gabata, ya aika saƙo ga Barcelona inda ya ce yana so ya sauya kwantiraginsa inda yake so a mayar masa da cewa zai iya barin kulob din ba tare da ya biya ko kwabo ba.
Sai dai kulob din ya bayyana cewa dole ne fa a biya euro miliyan 700 idan ana so Messi ya bar kulob dinsa.
A baya dai mahaifin Lionel Messi wanda kuma shi ne wakilinsa ya shaida wa La Liga cewa bai kamata a biya euro 700m (£624m) ba kafin dan wasan na Barcelona ya bar kungiyar.
A makon jiya ne dan wasan mai shekara 33 ya shaida wa kungiyar cewa yana so ya yi gaba bayan shekara 20 yana murza mata leda kuma ya yi amannar cewa zai bar kungiyar ba tare da biyan ko sisi ba.