Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi: Bai kamata a biya euro 700m ba kafin ɗan wasan ya bar Barcelona, in ji mahaifinsa
Mahaifin Lionel Messi wanda kuma shi ne wakilinsa ya shaida wa La Liga cewa bai kamata a biya euro 700m (£624m) ba kafin dan wasan na Barcelona ya bar kungiyar.
A makon jiya ne dan wasan mai shekara 33 ya shaida wa kungiyar cewa yana so ya yi gaba bayan shekara 20 yana murza mata leda kuma ya yi amannar cewa zai bar kungiyar ba tare da biyan ko sisi ba.
Jorge Messi ya bayyana a wata sanarwa cewa a karshen kakar wasan da ta wuce ne farashin da kungiyar ta dora a kan dansa ya kare.
Sai dai Liga ya yi raddi inda ta ce dole ya biya kudin kafin ta bar shi ya tafi wata kungiyar.
Kungiyar ta Sufaniya ta ce: "La Liga ta yi raddi kan sakon da ta samu daga daga wakilin Leo Messi.
"A cikin raddin, La Liga tana mai cewa su yi wa kwangilar bahaguwar fahimta. La Liga tana nanata sanarwar da ta wallafa ranar 30 ga watan Agusta."
A wasikar da mahaifin Messi ya aike ranar Juma'a, ya dage cewa kwangilar dansa ba ta fayyace ranar da Messi zai iya barin Barcelona ba, kawai dai ta ce dole ya bar kungiyar a karshen kakar wasa.
Ana kallon Manchester City a matsayin kungiyar da ta fi dacewa wurin daukar Messi idan ya bar Barca, kuma Mr Font, wanda ke fatan maye gurbin Josep Bartomeu a shugabancin kungiyar, ya yi amannar cewa akwai yiwuwar dan wasan ya tafi City domin yin aiki da tshohon kocinsa a Barca Barca Pep Guardiola.
Ya shaida wa BBC Sport cewa: "Babu abin da Messi yake so kamar yin gasa sannan ya yi nasara."