Mahaifin Messi na ci gaba da roƙa wa ɗansa gafara, Koulibaly zai tafi Manchester City

Mahaifin Lionel Messi ya kwashe kwana na biyu yana tattaunawa da Barcelona domin ta amince dansa ya bar kungiyar, kuma dan wasan Liverpool Andy Robertson ya ce yana fata dan wasan na Argentina mai shekara 33 ba zai tafi wata kungiyar da ke buga gasar Firimiya ba. (Sky Sports)

ShugabanNapoli Aurelio de Laurentiis ya ce yana son dauko dan wasan Arsenal dan kasar Girka mai shekara 32 Sokratis Papastathopoulos, matakin da zai bayar da dama ga dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, ya tafi Manchester City. (Standard)

De Laurentiis ya ce yana takaicin rashin sayar da Koulibaly mai shekara 29 a baya. (Manchester Evening News)

Dan wasanManchester Uniteddan kasar Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, na shirin komawa Roma gaba daya. (Mirror)

Monaco ta yi watsi da tayin da Manchester United ta yi mata na dauko dan wasanta mai shekara 19 dan kasar Faransa Benoit Badiashile, wanda ya ce zai ci gaba da zama a kungiyar. (Metro).

Manchester United na yunkurin kammala daidata albashin dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho da kuma kudin wakilinsa kafin ta bukaci dauko shi. (Star)

Sevilla tana ci gaba da fatan rike dan wasanReal Madrid Sergio Reguilon a matsayin aro zuwa kakar wasan da ke tafe duk da rahotannin da ke cewa dan wasan na Sufaniya mai shekara 23 na kan hanyarsa ta tafiyaManchester United. (Marca - in Spanish)

Arsenal na dab da kamala karbo arondan wasan Real Madrid da Sufaniya mai shekara 24 Dani Ceballos a karo na biyu a jere. (Mail)

Arsenal na duba yiwuwar dauko dan wasan West Ham da Brazil mai shekara 27 Felipe Anderson. (Football Insider)

Liverpool ba za ta sake bayar da aron dan wasan Wales mai shekara23 Harry Wilson ba duk da zawarcin da kungiyoyi irinsu Newcastle, Leeds da kuma Southamptonsuke yi masa. (Liverpool Echo)

An gaya waChelsea cewa dole ta biya akalla £30m idan tana son dauko golan Senegal Edouard Mendy, mai shekara 28, daga Rennes. (Telegraph)