Takarar gwarzon ɗan wasan PFA: An sanya sunayen Alexander-Arnold, De Bruyne, Henderson, Mane, Sterling, Van Dijk

'Yan wasan Liverpool hudu na cikin 'yan wasa shida da aka sanya sunayensu domin takarar gwarzon dan wasan shekara na Kungiyar Kwararrun 'yan Wasa ta bana.

'Yan wasan su ne Virgil van Dijk, Jordan Henderson, Sadio Mane da kuma Trent Alexander-Arnold.

'Yan wasan da ke fafatawa da su su ne 'yan kwallon Manchester City Kevin de Bruyne da Raheem Sterling.

Kazalika 'yan wasan Chelsea na cikin banagren mata da ke takarar gwarzuwar 'yar wasan Kungiyar Kwararrun 'yan Wasa ta bana.

Beth England, Sophie Ingle, Guro Reiten da kuma Ji So-yun na cikin 'yan wasan da ke takarar.

'Yar wasan da ke rike da kanbin Vivianne Miedema da kuma takwararta a Arsenal Kim Little na cikin jerin 'yan wasan da ke fafatawa.

Dan wasan Liverpool Alexander-Arnold na cikin 'yan wasan da ke fafatawa domin zama gwarzon dan wasan a rukunin matasa.

Wadanda ke fafatawa

Rukunin gwarzon dan wasan bana

Trent Alexander-Arnold - Liverpool

Kevin de Bruyne - Manchester City

Jordan Henderson - Liverpool

Sadio Mane- Liverpool

Raheem Sterling - Manchester City

Virgil van Dijk - Liverpool

Rukunin gwarzuwar 'yar wasan bana

Beth England - Chelsea

Sophie Ingle - Chelsea

Kim Little - Arsenal

Vivianne Miedema - Arsenal

Guro Reiten - Chelsea

Ji So-yun - Chelsea

Gwarzon dan wasan bana- Rukunin matasa

Tammy Abraham - Chelsea

Trent Alexander-Arnold - Liverpool

Marcus Rashford - Manchester United

Mason Greenwood - Manchester United

Mason Mount - Chelsea

Bukayo Saka - Arsenal

(Dole wadanda ke takara su kasance masu shekara 21 ko kasa da haka zuwa ranar 1 ga watan Yuli, 2019)

Gwarzuwar 'yar wasan bana- Rukunin matasa

Erin Cuthbert - Chelsea

Lauren Hemp - Manchester City

Chloe Kelly - Manchester City

Georgia Stanway - Manchester City

Lauren James - Manchester United

Ellie Roebuck - Manchester City